Ibtila'in fashewa a garin Appiate da rikicin kabilanci a garin Bawku, yarjejeniya da asusun lamuni na duniya (IMF), ce-ce-ku-cen tsige Ministan Kudi, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa. zanga-zangar kungiyoyin kwadago da na farar hula.
ACCRA, GHANA - Da kuma matsalolin tattalin arzikin kasar gaba daya ne suka yi tasiri a shekarar 2022 da muka yi bankwana da ita a Ghana.
A wannan shekara ta 2023, mashaharta sun bayyana wa Muryar Amurka burace-buracensu ga Ghana, inda suka yi hasashen samun sauki a bangarori daban daban, fiye da shekarar da gabata.
Masani a hulda tsakanin kasa da kasa da tsaro, Irbad Ibrahim ya ce yana da burin Ghana ta kasance kasa da ta fi kowacce zaman lafiya a Afirka sannan kuma gwamnati da kamfanoni su baiwa matasa aikin yi domin dakile fitar matasa zuwa kasashen waje.
.jpeg)
Comments
Post a Comment